Gamayyar kungiyar Arewa ta nemi gwamnatin tarayya ta yiwa ‘yan Bindiga Afuwa, inda ta caccaki gwamna El-Rufai da yace babu batun Sulhu
Kungiyar CNG ta nemi gwamnatin tarayya data goyawa Sheikh Gumi baya tare da baiwa ‘yan bindiga Afuwa.
Kakakin Kungiyar, Abdulaziz Sulaiman ne ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da manema labarai a jiya, inda yace suna kuma neman Fulani dake zaune a kudu, idan ba zasu samu tsaro a inda suke ba da su dawo Arewa.
Kungiyar tacs karbar yan Bindigar da suka tuba suka rungumi zaman lafiya abune me kyau. Ta kuma caccaki gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan matsayarsa ta cewa kada a yi sulhu da ‘yan Bindigar inda tace hakan zai kara kaiwa ne ga zubar da jini.