Kasar Amurika za ta sanya kafar Wando daya da Najeriya da sauran kasashen dake da dokokin hana Luwadi, Madugo da auren jinsi ta duniya (LGBTQI)
Shugaban kasar Amurika, Joe Biden, ya aike da takarda yana neman a kara karfafa bada dama ga ‘yan kungiyar Luwadi, Madugo da masu auren jinsi ta duniya.
Joe Biden, ya kuma yi barazanar sanya takunkumin tattalin arzigi da sanya dokar hana Visa ga kasar Najeriya da sauran kasashen da aka same su da laifin toye ‘yancin ‘yan Luwadi, Madugo da auren jinsi (LGBTQI).