An kaddamar da fara ginin hayar jirgin kasa ta Kano-Katsina-Maradi da kuma Kano-Dutse
A yau Talata aka kaddamar da fara aikin ginin hayar jirgin kasa da za ta taso daga Kano zuwa Katsina ta shiga Jibiya ta haura har Maradi Jumhoriyar Jihar.
Haka kuma da wadda za ta taso daga Kano zuwa Dutse ta jihar Jigawa.
An kaddamar da aikin hanyar jirgin ne yau Talata a Katsina.
Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, da na jihar Kano Abdullahi Ganduje gami da na Jigawa Badaru ne suka halarci taron kaddamar da titin dogon.
Akwai kuma Sarkin Katsina da na Kano da wakilan fadar shugaban kasa da dama da suka halarci shedar ginin titin jirgin
Za a iya tuna cewa Katsina Daily Post News ta wallafo maku cewa yau ne za a kaddamar da aikin hanyar jirgin da shugaban kasa Buhari ya ware ma makudan kudade don aiwatar da ita a cikin mulkinsa