Muhammadu Sanusi ll Ya Yaba A Kan Dakatar Da Kabara
Daga: Nuhu Umar Kankara
Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll ya maganta dangane da abin da ke faruwa tsakanin gwamnatin jahar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, inda ya ce da’awar malamin ba ta bisa kan hanya.
Ya yi wannan furuci ne a wajen karatun littafin Madarijus Salikheen na Ibn Qayyim Al-Jawziyya wanda ya gudanar a ranar Lahadi, 7 ga watan Fabrairu, 2021.
Sanusi ll ya yi bayani a kan abubuwan da ke faruwa a kano da fitintinu, inda ya roki Allah ya kawo mafita tare da yin kira ga al’umma da su kauce wa dukkanin abin da zai iya tayar da zaune tsaye.
Majiyar Daily episode HAUSA ta taruwaito cewa, kamar yadda wani bidiyon da aka dora a shafin twitter ya nuna, an jiyo tsohon sarkin na cewa Kano kasa ce da ta yi riko da koyarwar sunnah irin ta Shehu Danfodio, sannan ya shawarci kanawan da su tsaya kyam a kan abin da ya dora su a kai, wato tafarkin Ahlul Sunnah Wal Jama’a.
Malam Sanusi ll ya kara da cewa, matakin da gwamnati da malaman Kano suka dauka a kan Sheikh Kabara ya yi dai dai kuma abin a yaba ne, tare da rokon Allah ya tsare wa Kano da daukacin al’umma addininsu da akidunsu.