Tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo, ya fito fili ya fasa ƙwai dangane da halin ƙaka ni kayi da ƙuncin rayuwa da ‘yan Najeriya suka tsinci kansu a cik, inda ya tabbatar da cewar ‘yan Najeriya ne da kansu suka tsokano wahala da fitinar da suke ciki, amma ba gaskiya ba ne a rinƙa faɗin cewa wai Allah ne ya kawo.
Tsohon Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a sakonsa na sabuwar shekara ga ‘yan Najeriya, wanda ya saba yi a duk lokacin bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar Shekara a duk shekara.
Ya ce lokaci ya yi da shugabannin Najeriya za su mike tsaye wurin tabbatar da sun yi gyara akan yadda tattalin arzikin kasa ya tabarbare, da kuma tsamo ‘yan ƙasa daga cikin ƙangin Talauci da karayar arziki da suke ciki.
Tsohon Shugaban ƙasar ya ƙara da cewar wajibi ne su tsaya tsayin-daka wurin ganin sun kawo karshen rashin tsaro a Najeriya, saboda al’amarin kullum kara lalacewa yake yi, babu birni babu kauye musanman a karkashin wannan mulki na Buhari.
Ya yi kira ga gwamnati da su shiga harkar noma don tallafa wa kasa da samun cigaba a 2021. Wajibi ne a dage a gona don gudun kada ‘yan Najeriya su dinga kwana da yunwa.
Sannan ya kara da cewa, Najeriya tana bukatar addu’a, ta haka ne za a kawo karshen tashin hankalin da kasar nan take ciki. Sai dai ba addu’a kadai za a tsaya ba, wajibi ne a mike tsaye kuma a yi aiki tukuru.
Tabbas za a samu nasarar idan aka yi hakan a 2021, Ya kuma bayyana damuwarsa a kan rashin tsaro da kuma annobar COVID-19 mai kawo cikas ga tattalin arzikin kasa. Ya ce hakan ne babban kalubale, wanda ya janyo tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro.