Hukumar Lafiya ta Duniya ta kaddamar da gangamin yaki da shan taba sigari na shekarar 2021, inda ta wallafa sakwanni a kafofin sadarwar zamani da ke bayyana dalilai 100 na guje wa ta’ammali da sigarin.
Annobar coronavirus ta sanya miliyoyin masu shan taba sigari sun bayyana aniyarsu ta rabuwa da ita, lamarin da ya sa gangamin zai karkata ga taimaka wa mutane miliyan 100 wajen yin watsi da dabi’ar shan sigarin.
Shirin na Hukumar Lafiya ta Duniya zai samar da kyakkyawan yanayi ga masu bukatar barin shan tabar ta hanyar samar da ingantattun manunfofin yaki da mu’amala da sigarin tare da wayar da kan al’umma a game da dabarun da kamfanonin tabar ke amfani da su don rinjayar jama’a.
Hukumar Lafiya ta Duniya tare da kawayenta za ta samar da wani dandali a kafar intanet, inda dimbim al’umma za su samu bayanai masu amfani da za su kai su ga yin watsi da shan sigari a cikin harsuna da dama da suka hada da Ingilishi da Faransanci Sinanci da Larabci da sauransu.
Shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce masu amfani da taba sigari na bukatar kwarin gwiwar jingine dabi’ar zukar ta ganin yadda take sanadin mutuwar mutane miliyan 8 duk shekara.