Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Abdul’aziz Garba Gafasa da wasu yan majalisar guda 13 na Jam’iyyar APC na shirin komawa jam’iyyar PDP a jihar.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan tsohon kakakin majalisar ya ajiye aiki bisa radin kansa.
Jaridar Sahelian Times ta rawaito cewa, anyi zargin cewa Gwamna Ganduje ne ya shirya kawar da tsohon kakakin majalisar, wanda hakan ya sanya shi rubuta wasikar ajiye mukaminsa a ranar Talata.
ZIYARCI SHAFUKANMU NA FACEBOOK DA TWITTER