Rahotanni daga Bukur na Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato na cewa ana arangama tsakanin ƙabilun yankin.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa yanzu haka jami’an tsaro na harbi a sama domin tarwatsa matasan da ke jefe-jefe da duwatsu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Filato Uba Gabriel bai tabbatar da faruwar lamarin ba amma ya ce zai bincika.
An fara rikicin ne tsakanin al’ummar Hausawa da kuma sauran ƙabilun yankin bayan zargin juna da fara aikata kisa.
Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu…