Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, ya nuna ɓacin ransa sakamakon yadda Najeriya ta ƙara shiga halin karayar tattalin arziƙi.
A wani saƙo da Atikun ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa da a ce gwamnatin Najeriya ta ji irin shawarwarin da ya bayar da wasu shawarwarin masu kishin ƙasa, da tuni an guje wa faruwar hakan.
Idan bakumantaba jaridar DAILY EPISODE ta walafa cewa Najeriya Ta Afka Cikin Karayar Arziki Mafi Muni A Tarihi – Hukumar Kididdiga
Atiku Ya bayyana cewa ya bayar da shawarar Najeriya ta rage kuɗin da take kashewa wurin gudanar da mulki, da kuma tattalin kuɗin da ta rage kashewa domin guje wa ɓacin rana, haka kuma ya ce ya ba gwamnatin shawara da ta guji ciwo bashi.
A ranar Asabar ne dai Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce tattalin arziƙin ƙasar ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020, wanda hakan ke nufin tattalin arziƙin ƙasar ya samu karaya.
Atiku ya bayyana cewa duk da annobar korona ta jawo koma baya a ƙasar, akwai hanyar da ya kamata a ce an bi wurin guje wa afkuwar irin hakan ta hanyar amfani da hikima da basira wurin tafiyar da tattalin arziƙin ƙasar.
Ya kuma koka kan cewa Najeriya ba ta da kuɗin da za ta aiwatar da “ƙasaitaccen kasafin kuɗin ƙasar” inda ya ce a yanzu ƙasar na cikin halin talauci, kuma idan aka ci gaba a hakan ƙasar za ta karye baki ɗaya.