Gwamnatin Tarayya za fara tallafawa mutum 2640 yan jihar Katsina da da dubu hamsin-hamsin
Gwamnatin Tarayya ta fitar da ranar yau Talata a matsayin ranar ta fara bude manhanarta ta yanar gizo (portal) domin cikewa ta bayar da tallafin dubu hamsin-hamsin N50,000 ga kanana da matsakaitan yan kasuwa a duk fadin Nijeriya.
Ministar Kasuwanci da masana’antu ta Nijeriya kuma shugabar kwamitin bayar da tallafin Amb. Mariam Katagum ita ce ta bayyana hakan a ranar Jumu’a.
Maryam Katagum ta ce za a bude portal din ne daga karfe 11:59pm na ranar Talata 9 ga watan February har zuwa ranar Alhamis 18 February 2021.
Sanarwar ta bayyana cewa mutum dubu dari ne za su amfana da tallafin a duk fadin Nijeriya, inda jihar Lagos za ta sami kaso mafi tsoka na mutum 3,880, sai jihar Kano da mutum 3,280, da kuma jihar Abia da mutum 3,080 za su amfana da shirin.
Sauran jihohin Nijeriya kuwa, kowace jiha mutum 2,640 ne za su amfana da tallafin.
Dole kuma wanda zai amfana da tallafin ya kasance a nan cikin Nijeriya ne yake da tiredarsa, sannan kuma ya yi ma kasuwarsa rijista da satifiket din CAC, da kuma lambar asusun ajiya ta banki gami da BVN.
Sannan kuma dole a kalla masana’antar ta kasance tana da ma’aikata biyu, da kuma lambar rijista ta tantance abinci da magunguna NAFDAC
Sannan irin sana’o’i da ake bukata, da za a tallafamawa sune kamar masu hada takunkumin rufe fuska (Face mask) da sanadarin wanke hannu (hand sanitizer) da sabulun ruwa da sauran wasu kayan abinci masu gina jiki.
Ministar ta kuma bayyana cewa shirin sau daya kacal za a bayar da shi ga mutum dubu dari.
Domin shiga cikin shirin da za a fara yau Talata da karfe 11:59pm na daren yau, sai a shiga wannan adireshin nasu http://www.survivalfund.gov.ng