Masarautar Katsina ta dakatar da mai rike da sarautar gargajiya.
Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da Alhaji Samir Isma’ila Musawa a matsayin Sanyinan Katsina.
Dakatar da mai rike da mukamin ya kasance cikin wata sanarwa da sa hannun sakataren masarautar, Alhaji Bello M. Iffo (Sarkin Yakin Katsina) ya sanya wa manema labarai.

Sanarwar ta karanta a wani bangare “majalisar masarautar Katsina ta umurce ni da in yi rubutu kan dakatar da Alhaji Samir Isma’ila Musawa a matsayin Sanyinan Katsina”
Sai dai wasikar dakatarwar ba ta yi shiru ba kan dalilan dakatarwar.
Blueinknews ta tattaro cewa dakatarwar da aka yiwa Alhaji Samir ba za ta rasa nasaba da wani sauti na bidiyo ba inda aka ji Samir da ke takun saka yana wulakanta halayen wasu manya a jihar.
Tuni dai Samir ya musanta yin irin wannan kalaman na rashin mutunci ga wadanda lamarin ya shafa.