Amfanin Man Zaitun a Jikin Dan Adam
ZAITUN (OLIVE)
Shi dai zaitun ya kasance dangin ƴaƴan itace waɗanda suke da matuƙar amfani a jikin ɗan adam dalilin ire-iren sinadaran da suke ƙunshe dasu da kuma mai da suke samarwa wanda shima yana taka rawar gani wajen magance cututtuka na fata da na cikin jiki. Asali ma zaitun yana ɗaƴa daga cikin itatuwan da ALLAH (SWT) ya ambata a cikin Alƙur’ani mai girma a wajaje da dama tare da muhimmancin su.
Mafi yawancin alfanun shi zaitun ana ribatar sa daga cikin man zaitun ɗin. Man zaitun ana fitar dashi ne daga ɗanƴen ƴaƴan zaitun har ma da nunannu wanda a wajen fitar da man wani akan tsuma shi wani kuma a dafa shi. Man zaitun ya rabu zuwa kashi biyu:
– Virgin Olive oil: wanda aka fitar daga ɗanyen zaitun ta hanyar gargajiya ko zamani amma batare da an matsa wajen kalacewa gabaki ɗaya ba saboda a tabbatar da ingancin shi. Saboda ingancin shi ya sa dashi aka fi amfani wajen yin magani da sauran amfani kamar wajen girke-girke. Shi ‘Virgin olive oil’ ya kasu zuwa mataƙai uku na inganci:
Extra virgin olive oil (mafi inganci)
Fine virgin olive oil (mai matsakaicin inganci)
Semi-fine virgin olive oil.
– Olive Pomace oil: wanda aka fitar dashi ta hanyar zamani kuma ya kasance an kalace gabaki ɗayan man dake ciki. A wasu wuraren ma ya kasance sai bayan gama fitar da ‘Virgin olive oil’ daga zaitun sai a fitar da ‘Olive pomace oil’ daga totuwar/sauran.
AMFANIN MAN ZAITUN A JIKIN DAN ADAM.
1. Kariya daga kamuwa da cutar daji (Cancer): Binciken masana ya nuna cewar man zaitun yana ƙunshe da sinadarin ‘antioxidants’, ‘lignan’, da ‘squalene’ waɗanda suke rage ko kawar da abin dake kawo cutar daji. Haka man zaitun kan taimaka wajen kare waɗanda suka taɓa kamuwa da cutar daji daga sake kamuwa.
2. Rage ƙiba: Man zaitun yana ƙunshe da sinadarin ‘oleic acid’ wanda kan taimaka wajen ƙona kitse da rage ƙiba.
3. Magance ciwon sukari (Diabetes): Binciken cibiyoyi da dama na masana ya tabbatar da cewar man zaitun yana da matuƙar tasiri wajen rage kamuwa da ciwon sukari ta hanyar sanya kuzari ga sinadarin dake rage sukari a cikin jini (Insulin).
4. Narkar da abinci: Man zaitun na taimakawa wajen saurin narkar da abincin da akaci.
5. Ciwon gaɓoɓi: Man zaitun yana taimakawa wajen magance ciwo da kumburin gaɓoɓi ko amosanin gaɓɓai (Rheumatoid arthritis). Amfanin shi wajen ciwon gaɓoɓin yafi tasiri idan aka haɗa da man kifi.
6. Cutar mantau (alzhiemer disease): Man zaitun na taimakawa wajen maganin cutar mantau a wani bincike wanda ana nan kan yinshi.
7. Bugun jini ko cutar shanyewar ɓarin jiki (Stroke): Bincike ya nuna cewa mafi yawancin mutane masu amfani da man zaitun yau da kullum ba a cika samunsu da shanyewar ɓarin jiki ba.
8. Rage kumburi (na ciwo): Man zaitun yana matuƙar taimakawa wajen rage kumburi saboda sinadarin ‘oleic acid’ da kuma ‘antioxidant’ (oleocanthal).
9. Man zaitun ya kasance yana da matuƙar amfani wajen girke girke sakamakon ya ƙunshi ‘monounsaturated fatty acid’ wato ‘oleic acid’ baya daskarewa.
10. Gyaran jiki da gashi: Matuƙar kana fama da matsalar zubar gashi da lalacewarsa, yawaita amfani da man zaitun, saboda ‘vitamins’ da sindaran ‘antioxidant’ dake cikin sa waɗanda suke taimakawa wajen haɓɓaka sumar kai da inganta shi, sannan ya kareta daga zubewa nan gaba.
11. Gyaran fata: Haka kuma man zaitun na samar da sinadaran ‘vitamin A’ da ‘vitamin E’ waɗanda dukkanin su ingantattu ne wajen gyara lafiyar fata ta zama sumul tayi laushi.
12. Magance ciwon zuciya: Bincike da dama da manazarta suka gudanar sun tabbatar da cewa yawaita amfani da man zaitun na rage bugun jini a zuciya, saboda sinadaran dake cikin man zaitun na tocopherol, polyphenols, da kuma wasu sinadaran da suke taimakawa zuciya ta numfasa.
13. Haka kuma man zaitun a jiki yana rage yawan ‘Cholesterol’ a jikin manyan mutane (tsofaffi) tare da ƙara kare lafiyar jikinsu.
14. Haƙiƙa man zaitun yana maganin cututtukan da mutum bai san suna jikin sa ba, sannan idan mutum yanayin amfani da man zaitun don saduwa da iyali to riba biyu ce fa; ga magani ga lada.