Kotun tafi da gidanka da gwamnati Kano ta kafa don hukunta wadanda suka karya dokar zaman Gida Dole da gwamnatin Tarayya ta saka a Kano ta kama wasu limamai biyu da laifin karya doka.
Su dai wadannan limamai sun karya dokar hana yin Jam’i a masallatai da aka saka saboda dakile yaduwar Coronavirus a jihar.
Limaman da mazauna karamar Hukumar Minjibir ne, sun yi fatali da dokar hana sallar jam’i, suka tara jama’a suka ci gaba da sallolin su.
Bayan shara da zasu rika yi har na sati daya, za kuma su biya naira 10,000 kudin tara.
Baba Jibo-Ibrahim, wadda shine Kakakin ma’aikatan Shari’a na jihar Kano ya shaida wa manema labarai cewa gwamna Abdullahi Ganduje ya Kama wasu manyan motoci da kansa suna kokarin shiga Kano. ” An ci taran kowannen taran naira 150,000.”
Sannan kuma an cafke wata mata ita ma da ta yi wa jami’an tsaro rashin kunya. An yanke mata hukuncin share furzin na Sati daya.
Bayan haka kuma an kama wani da yayi dambe da dan sanda ya kacaccala masa kaya sannan ya rika karyar cewa shi ma dan sanda ne kuma ma yana gaba da jami’in a aikin.
Daga baya ashe karya yake yi. Tuni dai an tasa keyar sa zuwa hedikwatar ‘yan sandan Kano domin yin bincike akai.