Cikin ‘yan Kwanakin nan ne rashin fahimta ya kunno kai tsakanin sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Uba Sani da kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, inda rikicin siyasar ke kara daukar sabon salo. Manyan ‘yan siyasan biyu sun fito ne daga yankin mazabar Kaduna ta tsakiya.
Masana sun bayyana ‘yan siyasar biyu da cewa suna gwagwarmaya ne ta neman daukaka da iko a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shiyyar.
Yankin sanata na tsakiya, wanda Uba Sani ke wakilta, ya hada da kananan hukumomin Birnin Gwari, Chikun, Giwa, Igabi, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu da kuma Kajuru. Zailani daga wannan yanki yake kuma yana wakiltar mazabar Igabi.
Kakakin majalisar dokokin a baya-bayan
nan ya zargi Sanata Uba Sani da rashin tabuka wani abin a-zo-a-gani a yankin mazabarsa ta Igabi.
Uba Sani, wanda tsohon babban mataimaki ne na musamman ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, an ce yana sa ido ne a kujerar mulkin Kaduna a zaben 2023 mai zuwa.
Zailani, wanda ya zama kakakin majalisar jihar a ranar 25 ga Fabrairu, 2020, masu lura suna cewa shi ma yana harin kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a zaben 2023 mai zuwa.
Sai dai masu sukar Sani, sun ce ba za a amince da shi ba, saboda ya ci amanar abokinsa na kusa, Shehu Sani don burin kansa na siyasa.
Suna ganin shi a matsayin wanda ba shi da cikakken matsayi a siyasance, kasancewarsa wanda ya ci gaba da dogaro da Gwamna El-Rufai don share fagen harkar siyasar sa.
Tuni, jita-jita ta fara daga wadanda ke kusa da sansanin Uba Sani cewa idan gwamnan ya gaza amincewa da burinsa na gwamna, zai iya daukar damar sa a cikin sansanin tsohon Gwamna Ahmed Markarfi don komawa jam’iyyar PDP.
“Idan har APC ta hana shi tikiti, Sani zai bukaci tabbaci daga PDP da Makarfi kafin ya yi irin wannan kasada, amma mutane daga sansaninsa suna ta kai kawo, ”in ji wata majiya da ke kusa da sansanin.
Kakakin majalisa Zailani, a daya bangaren, ya kasance mai kaifin kishin talakawa tsawon shekaru kuma ya kasance dan majalisa a karo na hudu.
Zailani, wanda a yanzu shi ne shugaba, kungiyar masu magana da yawun Arewa, an ce yana da tunanin kansa, kuma masu lura da al’amuran siyasa na cewa yanayin halayyarsa ta sa ya kasance mai cin gashin kansa.
Kodayake dimbin matasa daga mazabarsa suna kaunarsa, amma masu adawa da Zailani suna yi masa kallon tuhuma, inda wasu ke cewa, “har ma gwamnan ba zai iya hango shi da sauri ba.”
Wasu majiyoyi daga cikin APC a jihar sun shaida wa Aminiya a ranar Lahadi cewa yayin da Gwamna El-Rufai ya dukufa kan mayar da hankali kan shugabanci da kuma share hanyar da zai cimma burinsa na nan gaba, ga alama akwai rikici a cikin gidan siyasarsa.
Wasu kuma na ikirarin El-Rufai da kansa na iya kasancewa a bayan yunkurin Zailani na kawar da burin Sani kamar yadda suke ikirarin cewa gwamnan ya nuna shakku kan sanatan na iya shugabantan jihar.