Abin baƙin ciki da alhini ya samu jam’iyya mai Mulki ta APC inda ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta a Shiyyar Kudu maso yammacin Najeriya, mai suna Mista Samuel Ojebode.
Tuni Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta hannun mai magana da yawun shi Femi Adesina ya aike da saƙon ta’aziya ga iyalai da ‘ya’yan jam’iyyar APC bisa ga wannan babban rashi da ya faru.
Ojebode, wanda ya kasance jigon APC a jihar Oyo, ya rasu a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, yana da shekaru 87 a duniya. A wani sakon ta’aziyya, da wani sanata daga jihar, Teslim Folarin ya wallafa, ya nuna bakin cikinsa, da kiɗimewa akan wannan rashi.
A wani jawabi daga Yakeeen Olaniyi a Ibadan, Folarin ya bayyana mutuwar a matsayin wani babban asara ga ahlin APC a Najeriya.
Folarin ya bayyana cewa jigon na APC ya shirya taro na lumana mai cike da nasara ga ‘ya’yan jam’iyyar a mazabar Oyo ta tarayya.
Ya ƙara da cewar Ojebode ya kasance shugaba abun koyi, mai mutunci da kima.
A sakon ta’aziyyar shi Farfesa Adeolu Akande, Shugaban hukumar NCC, ya yi ta’aziyya ga iyalai, abokai da ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar kan wannan rashi.