Kungiyar dattawan arewa ta yi zargin cewa Inyamurai ne ke aiwatar da mafi akasarin hare-hare da ake kai wa ‘yan arewa, musanman a sashin Kudancin ƙasar.
An ruwaito cewa Shugaban kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi, ne yayi zargin a ranar Talata, 8 ga watan Disamba, Fatakwal jihar Ribas.
A cewar rahoton, shugabannin na Dattawan Arewa na wani rangadi ga al’umman arewa a fadin kasar biyo byan zanga-zangar EndSARS.
Ya bayyana karara cewa mafi akasarin farmakin da ake kaiwa ‘yan arewa a yankuna daban daban na kudu yana fitowa ne daga wajen mutanen jihohin kudu maso gabas, wato Tsagerun Inyamurai.
A wani lamari makamancin haka, Kungiyar matasan tare ta NYLF na kasa, tayi gargadin cewa ta sanar da mambobinta a fadin jihohin arewacin Najeriya da Abuja, kan su shirya yin gaba-da-gaba da duk wasu mutane da suka shirya zanga zangar EndSARS na biyu.
Kungiyar ta ce zanga zangar ta kere fa’idarta, cewa ba za ta zuba ido ta kyale wasu su jefa yan Najeriya cikin wani kangin rayuwa ba a yayinda ake tsaka da matsin tattalin arziki.
Shugaban kungiyar na kasa, Kwamrad Elliot Afiyo ya ce bata gari sun kwace rukunin farko na zanga zangar wanda ya jefa kasar cikin koma bayan tattalin arziki, inda ya kara da cewa NYLF ba za ta bari a maimaita wani zanga zanga ba a jihohin arewa 19.
A shirts muke mu bada dukkan goyon bayan da zamu iya domin hana ‘yan iska tada zaune tsaye.
mudai muna kira da aji tsoron allah adaina wanna kashen kashen kuma muna kirada baban murya shugaban kasan nageria yema shaani tsaro garanbawul yanemi yara masu jini ajika