Gwamnan Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin rufe baki da hanci miliyan daya a jihar da zummar dakile cutar korona.
Gwamna, wanda ya kaddamar da bayar da takunkumin ranar Litinin a Kano, ya ce akwai bukatar mazauna jihar su dauki karin matakai na kula da lafiyarsu a wannan lokaci da cutar korona take ci gaba da addabar duniya.
Ya ce za a raba makarin fuskar ne a kananan hukumomi takwas da ke kwaryar birnin Kano, yana mai shan alwashin hukunta duk wanda aka kama ba tare da sanya makarin fuskar ba.
Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa ta dauki mutanen da ta kira ‘dakarun tsafta’ wadanda za su yi yaki da cutar korona.
“Daukarku wannan aiki da aka yi, an yi tunanin kwarai da gaske; aka zabo matasa, maza da mata, masu jini a jiki wadanda za su shiga lungu-lungu da kasuwanni…a tabbata cewa an yi safta yadda ya kamata,” in ji Gwamna Ganduje.