Yayin da kowanne dan siyasa yake shiri akan zaben shugaban kasa na 2023, jam’iyyar APC ba a barta a baya ba, sai dai alamun nasara suna ta harararta don yanzu haka gwamnoni 4 na jam’iyyar PDP sun shirya tsaf akan sauya shekarsu zuwa APC.
A ranar Litinin ne aka samu labarin yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya lallaba har babban birnin tarayya, Abuja don tattaunawa da shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.
Wani mai fadi a ji na jam’iyyar APC ya sanar da Punch cewa gaskiya ne batun zuwan Fani-Kayode wurin shugabannin jam’iyya, duk da dai tsohon ministan bai riga ya fadi wata magana ba tukunna.
Majiyar ta tabbatar da yadda haduwarsu ta haifar da da mai ido. Kamar yadda yace, “Fani-Kayode ya samu Yahaya Bello da Buni a Abuja a ranar Lahadi, sun tattauna na tsawon sa’o’i 2 akan siyasar 2023 da kuma yadda APC take gudanar da rijistar ‘yan jam’iyya.”
Da aka tambaye shi akan gwamnonin PDP 4 da suke shirin sauya sheka, cewa yayi ba zai bayyana ba saboda hakan ya zama rashin wayau.
Kamar yadda yace, “Gwamnonin guda 4 suna so su samu tabbacin cewa idan sun canja jam’iyya za a iya basu damar tsayawa takara a jihohinsu. Wannan ne dalilin da ya sanya aketa tattaunawa dasu.”