Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi takaicin faruwar wani rikici da ya barke tsakanin Yarabawa da Hausawa a Fagba, yankin Ifako-Ijaiye da ke jihar.
Bayan Sanwo-Olu ya kai ziyara wuraren ne a ranar Talata, ya lashi takobin hukunta duk wadanda ya gano suna da hannu a cikin rigimar, da kuma biyan diyyar ɓarnar da aka yi.
Ya tabbatar wa da mazauna wurin, wadanda rikicin ya shafa cewa zai share hawayensu, kuma zai yi tsayuwa irin ta mai daka wajen ganin ya kare rayuka da dukiyoyinsu.
Gwamnan dya samu rakiyar mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat, sakataren gwamnatin jihar, Folasade Jaji, mai bai wa gwamnan shawara a harkar ilimi, Tokumbo Wahab da shugaban ma’aikata, Hakeem Muri-Okunola.
A cewarsa, “Irin asarar da na gani a wurin nan ta kazanta. Don haka za mu fara bincike take-yanke, a kan lamarin. Shugabannin unguwannin za su zauna su rubuta sunayen wadanda aka barnatar wa da dukiya.
“Muna so mu yi amfani da wannan damar wurin fadakar da bata-gari da ke kusa, don sannu a hankali za mu gano su. “Idan mutum ya san bashi da wani aikin yi ko kuma yana cikin wadanda suka assasa rikicinnan, wannan ne jan kunne na karshe.”
“Gwamnati za ta yi bakin kokarinta wurin biyan asarar, kuma masu shaguna su ji tsoron Allah yayin rubuta asarorinsu.”