Gwamnan jihar Ribas a Najeriya, Nyesom Wike ya bayyana kungiyar ‘yan awaren kabilar Ibo, IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, kuma ya sanya hannu a wata doka da ke haramta ta da ayyukanta a jihar.
Wannan matakin na kunshe ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun mai taimaka wa gwamnan na musamman a harkokin hulda da kafafen yada labrai, Kelvin Ebiri.
Eiri ya bayyana cewa, a wani jawabi da gwamna Wike ya gabatar ga al’ummar jiharsa a daren Laraba a Fatakwal, ya jaddada cewa jihar Ribas dai gida ne ga dukkanin ‘yan Najeriya daga kowace kabila.
Ya ce gwamnatinsa tana alfahari da gudummawar da wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ke bayarwa a fannoni dabam dabam da suka hada da tattalin arziki da zamantakewa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnatin jihar Ribas ba za ta lamunci wata kungiya daga ciki da wajen jihar da za ta tayar da zaune tsaye da zai kai ga rasa rayuka da dukiya ba, tana mai cewa, gwamnatin jihar na tir da ayyukan IPOB, kuma hakan ba yana nufin tana gaba da wata kabila bace, saboda za ta ci gaba da huldar alkahiri da dukkan kabilun dake jihar.