Majalisar dokoki ta ƙasa ta nemi Gwamnatin tarayya ta dakatar da batun komawar dalibai Makarantu har zuwa nan da watanni uku masu zuwa, domin ganin abin da ka iya zuwa ya dawo akan batun yaƙi da cutar CORONA.
Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere, ya ce gwamnatin tarayya ba ta tuntuɓi sauran masu ruwa da tsaki kafin ta bada sanarwar komawar dalibai makarantu ba.
Kwanan watan buɗe makarantu na ranar Litinin,18 ga watan Junairu, ya jawo cece-kuce sakamakon gaggawar shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke, inda suka ce akwai haɗari a bude makarantu saboda Annobar COVID-19.
Da yake maida martani akan buɗe makarantu ranar 18 ga watan Junairu, Honarabul Julius Ihonvbere, shugaban kwamitin majalisa akan ilimi yace buɗe makarantu babbar barazana ce ga yaƙi da annobar COVID-19 a karo na biyu.
Ihonvbere ya ce Gwamnatin Tarayya bata tuntuɓi majalisa ba kafin yanke shawarar cewa dalibai zasu kara komawa makarantu ranar 18 ga wata ba.
Ya ƙara da cewa a dakatar da komawa makarantun zuwa nan da watanni uku don ganin yadda hali zai yi, ya kuma koka akan rashin “daukar mataki ko wani shirin kare ɗalibai daga annobar COVID-19.
“Duk da kasancewar makarantu a rufe suke, ana samun mutane 500 zuwa 1000, ina kuma ga ace an buɗe makarantu. “Akan me ake gaggawar buɗe makarantu ba tare da daukar matakan kariya ko wani shiri akan kare rayuwar ƴa’ƴanmu ba?
“Basu tuntuɓe mu ba, ya kamata aƙalla ace sun tuntuɓi kwamitin mu, ba wanda ya tuntuɓemu koda daga ma’aikatar ilimi ne,” a cewar Dan majalisar.