Ministar kudi, Zainab Ahmad ta ce gwamnati na shirin cike wannan gibi ta hanyar ranto kudi daga ciki da wajen kasar nan, da kuma kudin da za’a samu daga sayar da kadarorin gwamnati.
Sake nazarin ya zo ne a daidai lokacin da aka samu akasi game da hasashen da gwamnatin tarayya ta yin a kudaden da take ganin za ta samu a shekarar, amma COVID-19 ya kawo cikas.
Shugaban BPE, Alex Okoh ya tabbatar da sake nazarin tsarin, inda yace hakan ya zama dole domin su san wani ciniki ne zai kammalu a shekarar 2020 duba da matsalar COVID-19 ta haifar.
Kafin bullar COVID-19, BPE ta yi hasashen samun N266.8bn daga sayar da kadarorin gwamnati, inda za ta kashe N3.9bn wajen gudanar da cinikayyar, za ta mika ma gwamnati N266.8bn.
Daga cikin cinikayyar da BPE za ta tara wadannan kudade akwai wanda suka fara tun a 2019 da suka hada da kammala cinikin tashar wutar lantarki ta Yola, da Afam Power Limited.
A wani labari kuma, A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin ciyar da dalibai daga gidajen iyayensu duk da cewa ba’a bude makarantu a Najeriya ba.
Punch ta ruwaito an kaddamar da ciyarwar ne a wata makarantar firamri dake garin Kuje a babban birnin tarayya Abuja, Central Science Primary School. Ministar kula da bala’o’i da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouk ce ta kaddamar da aikin, inda tace gwamnati na kashe daruruwan miliyoyi a duk rana don ciyar da daliban.