Bara Ba Addini Bane – Amina Lawal Dauda
Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta tallafi mata 3,400 da kudade domin su kama ko habbaka sana’o’in hannu.
Hakan, kamar yadda mai ba gwamnan jihar shawara kan ilmin ‘ya’ya mata da bunkasa rayuwar kananan yara Haj Amina Lawal Dauda ta ce, zai taimaka wa matan su dauki nauyin kananan ko marayun da gare su.
A wajen ba da tallafin da ya gudana a Daura, Haj Amina Lawal Dauda ta ce babban burin gwamnatin Gwamna Masari, shi ne ta ga kowa ya tsaya da kafafunsa, ba tare da yawon barace-barace ko na maula ba.
Ta ce babu mutunci a tusa keyar yara kanana ana yawon bara da su, hakan kamar yadda ta ce, shi ne ummul-aba’isin gurbacewar tarbiyyar yaran.