Rahotanni daga ƙetare na bayyana cewa kasar Faransa ta sha alwashin ɗaura ɗamarar yaki da akidun addinin Islama, da niyyar ganin bayan Addinin Musulunci baki ɗaya.
Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Gerald Darmanin, ne ya bayyana hakan bayan kisan wasu mutane uku a wani Coci da ke Nice yankin kudancin ƙasar, kamar yadda sashin Hausa na gidan Rediyon BBC ya ruwaito.
Darmanin ya yi gargadin kara samun irin wadannan hare-hare, sannan ya jaddada cewa kasar Faransa ba zata zuba ido tana kallon waɗanda ya kira ‘yan ta’adda suna keta hakkin jama’a masu ‘yanci ba.
Anata ɓangaren Shugabar masu adawa a kasar, Marine Le Pen ta yi kira ga gwamnati a kan ta samar da dokokin gaggawa domin tasa keyar masu kaifin kishin Islama zuwa kasashensu na asali.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron zai sake kiran wani taro na majalisar tsaro domin tattauna batun harin na Nice da kullen COVID-19, wanda ya fara aiki da tsakar dare. A yanzu haka, wanda ake zargi da kisan na birnin Nice na cikin mawuyacin hali a asibiti bayan jami’an ‘yan sanda sun harbe shi.
Don Samun Ingantatun Labarai Kuziyarci Shafin Mu FACEBOOK & TWITTER