Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan yan sanda Sanusi Buba ta yi nasarar kama mutane biyu a karamar hukumar Dutsinma, ta jihar Katsina, wadanda ke baiwa yan bindiga bayanan sirrin domin aikata ta’addanci ko kuma yin garkuwa da mutanen.
Wadanda aka kama sun hada Bilyaminu Ma’aruf, dan shekara talatin da biyar da haihuwa, da ke zaune a Unguwar Kadangarun Dutsinma da kuma Sani Umar dan shekara arba’in da haihuwa, da ke zaune a garin Gammo dake karamar hukumar Dutsinma.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Gambo Isa ya yi baje-kolin su ga manema labarai, a helkwatar rundunar da ke Katsina. Inda ya ce sun shahara wajen ba da bayanan ga barayin daji.
A cikin binciken dukkan su sun amsa laifin su, kuma su ne suka kitsa satar mutane da dama a cikin garin Dutsinma, ciki har da satar wata mata, Aminu Usman, yar shekara ashirin, wadda aka biya naira dubu dari tara ciki har an ba su dubu ashirin.