Shin ko kasan yadda zakayi idan kayi rafkanuwa a Sallah?
A lokuta da dama mutane sukanyi rafkanuwa a Sallah sannan suyi ta tunanin ya za’ayi su gyara wannan Sallah, Wasu har sun kan sake wannan Sallah to amma ga wasu bayanai da zasu taimaka ma wanda yayi rafkanuwa ya gyara wannan Sallah tasa.
Da farko dai idan yayi ragi a Sallah to zaiyi Sujada Qabli haka kuma idan yayi kari zai Sujada Ba’adi, to ko yaya akeyin Sujada Qabli da Ba’adi? Ku biyo ni.
Yadda ake yin sujjada Qabli da Ba’adai shine:
Idan sujjada Qabli ne to bayan mutum yayi tahiyar karshe kafin sallama sai mutum yayi sujjada guda biyu, sannan idan yayi sujjadar sai ya sallame wannan sujjada Qabli kenan, idan kuma sujjada ba’adi ce to ita ana yinta ne bayan anyi sallama daga sallah sai kayi raka’a biyu sai ka sallame.
Akwai yanayiyyika da suke faruwa na yin mantuwa a cikin sallah wanda hakan yake haifar da yin Qabli ko Ba’adi
Dukkan abinda zai faru na yin ragi a cikin sallah to ana yi masa sujjada Qabli. Idan abinda ya faru bangaren kari ne a cikin sallah to shi kuma za’ayi masa sujjada ba’adi.
Wanda yayi ragi kuma yayi kari duk a cikin sallah daya to shi kuma zaiyi sujjada Qabli. Wanda ya ya bayyana karatun sallah a wajen da ake boyewa zaiyi sujjada ba’adi. Wanda kuma ya boye karatun sallarsa wajen da ake bayyana karatu to shi zaiyi sujjada Qabli. Wanda ya kara raka’a daya ko raka’a biyu a cikin sallah to shima Zaiyi sujjada ba’adi. Wanda yayi raka’a biyu sai yayi sallama bayan kuma ba sallar asuba yake yi ba to shima zaiyi sujjada ba’adi.
Wanda kuma ya kara ra’ka’o’i dai dai da raka’ar sallar da yake yi to sallarsa ta baci sai dai ya sake sabuwa, misali mutum ya kara raka’a Hudu a cikin sallar Azahar ko raka’a biyu a cikin sallar Asubah to sallarsa ta lalace amma idan raka’o’in da ya kara basu kai adadin raka’ar sallar da yake yi ba to sallarsa bata lalace ba sai dai zai yi sujjada ba’adi (bayan sallama).
Wanda ya karanta sura biyu ko fiye da haka a cikin raka’a daya to babu komai a kansa, haka idan ya fara karatun sura bai karasa ba koda aya daya ya karanta a cikin surar to babu komai hakan ma daidai ne, idan ma mutum yana karanta wata surar ya manta ya koma cikin wata surar daban to babu komai sallah tayi daidai.
Wanda yayi kokwanton kan ko sallarsa ta cika ko bata cika ba to kawai yabarta a matsayin bata cika ba, idan yana tunanin raka’a 3 yayi ko 4 to sai ya ciko daya dan ta zama hudu sannan yayi Sujada Qabli bayan tahiya sannan ya sallame.
Alhamdulillah Allah yasa mu dace.