KAITSAYE DAGA BABBAR KOTUN JIHAR KATSINA (KATSINA STATE HIGH COURT)
A yau Ake sharia tsakanin Maslaha Motors Katsina, Nigerian Custom Service
A yau 11/05/2020 za’a fara sauraren karar da Kamfanin Sayar da mota na Maslaha Motors Katsina, dake jihar Katsina ya shigar gaban babbar kotun jihar Katsina (Katsina State High Court Of Justice) kan hukumar yaki da fasa kwabri ta kasa (Nigerian Custom Service) .
Kamfanin Masala Motors yana karar Hukumar yaki da fasa Kwabri ta kasa da kin basu damar biyan kudaden da aka nemi kamfanin ya biya na tara da aka sanya mashi, wanda suka kai kimanin Naira miliyan saba’in da hudu (#74,000,000) saima kokarin cin mutunci da hukumar take kokarin yi ga kamfanin. Bayan Kulle Kamfanin da hukumar tayi tun ranar July, 24, 2019.
Babban Daraktan Kamfanin Alh *Shuaibu Muhammadu* shine yake wakiltar kamfanin a zaman kotun . Kubiyomu zamu kawo maku labarin kaitsaye na yadda zaman kotun ya kasance na yau.
Abubakar Shafi’i Alolo
Director General
Mobile Media Crew
11/05/2020