An gudanar da jana’izar shahararren dan kwallon duniya na kasar Argentina Diego Armando Maradona.
An rufe Maradona kusa da mahaifansa a makabartar Bella Vista da ke wajen Buenos Aires.
To sai dai an samu turmutsutsi, bayan da dubbai suka yi jerin gwano don ganin gawar a fadar shugaban kasa.
Daga karshe sai da ‘yan sanda suka bada hayaki mai sa hawaye, su ka kuma canza wa akwatin gawar Maradona wuri, bayan da jama’a suka balla kofar dakin da ta ke ajiye ta don yi masa ganin karshe.
Diego Maradona ya mutu ne a ranar Laraba yana da shekaru 60, bayan da ya samu bugun zuciya.
A saƙon da ta wallafa a shafin Twitter, hukumar ƙwallon ƙafar Argentina ta bayyana “matuƙar baƙin cikinta bisa mutuwar gwarzonmu”, tana mai ƙara wa da cewa: “Za ka ci gabada kasancewa a zukatanmu.”
Ɗan ƙwallon Argentina da Barcelona Lionel Messi ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Maradona, yana mai cewa shi “Mahadi ne mai dogon zamani”.
“Wannan ranar matuƙar baƙin ciki ce ga dukkan ‘yan ƙasar Argentina da masu son ƙwallon ƙafa,” in ji Messi. “Ya bar mu amma yana raye saboda Diego Mahadi ne.”