Aliyu Abdullahi Obobo Yadake Daurar Aniyar zuwa Saudiyya akan Keke.
.
Mutumin nan mai suna Aliyu Abdullahi Obobo wanda yayi niyar tafiya kasar Saudiya a Keke shekarar da ta gabata, ya sake daurar aniyar a yau Mal. Aminu Iliyasu Kala ya zanta da shi bayan ya sake daura sirdin kekensa domin tafiya kasar Saudiya.
A cikin zantawarsa da Mal. Aminu, ya tabbatar masa da cewa wancan yunkurin da yayi na tafiya bai yiwu bane saboda jami’an kula da shege da ficce na kasa da kasa sun kamashi a kasar Chadi suka tuhume shi a kan cewa bayada Katin Zirga zirga a tsakanin ƙasashe wato International passport shine ya dawo domin ya mallaki passport din kuma yanzu ya samu ya mallaki nashi.
Sannan ya samu daidaito da mahaifin Matarsa wanda ya fito gidan radio ya bayyana rashin amincewarsa, yanzu sun daidaita kuma sunyi masa fatan nasara.
Abin mamaki da Malam Aliyu Obobo shine akwai mutane biyu da suka dauki zunzurutun kudi har Naira Milyan Daya da Dubu Dari Bakwai suka bashi domin ya hakura da tafiya a keke ya hau jirgi, haka mutumin nan yaki karba domin yace shi burinsa ya tafi kasar Saudiya akan keke.
Muna yi masa fatan alkhairi, Allah ya kaishi lafiya ya kare shi dukkan Sharri a hanya Amin.
Muhammad Sanee Bauchi.