Ƙungiyar Gwamnonin jihohin arewa 19 sun ce a shirye suke da su saurari koken matasan yankin a kan matsalolin da suke fuskanta, ko suke addabar su.
Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Simon Lalong, ya fadi hakan a ranar Laraba a Kaduna yayin taron rantsarwar kwamitin matasa, wacce aka kirkira musamman don samar da mafita ga yankin.
A wata takarda da jami’in hulda da jama’ar gwamnan, Macham Makut ya saki, ya ce wajibi ne samar da ayyukan yi, kawar da jahilci, ta’addanci da talauci ga matasa ta hanyar kirkirar kwamiti.
A cewarsa, an kirkiri kwamitin, wacce Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli yake jagoranta, sakamakon taron da masu ruwa da tsakin arewa suka yi, domin samar da mafita a Arewa.
A cewar Lalong, “Matasa sun fi kowa yawa a kasar nan, don haka su ne masu ruwa da tsaki a kasar nan. “Wajibi ne a sauraresu, kuma a yi amfani da shawarwarinsu don tafiyar da mulki yadda ya kamata.
“Wajibi ne a matsayinmu na shugabanni mu janyo matasa a jikinmu, don sanin matsalolinsu.”
Anashi bayanin Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya tabbatar da cewa kwamitin zai tabbatar da cewa an dage wurin tallafawa da taimaka wa matasa.