Rana ta biyu a Garin Dikwa Zulum ya Raba kuɗi, da Abinci a Dikwa.
Maigirma Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya je garin Dikwa don sanya ido kan rabon kuɗi da kayayyakin abinci ga mutum 34,000.
Gwamna Zulum ya kai ziyara garin Dikwa ne a jiya Alhamis kafin yau ya jagoranci rarraba kudi da kayan Abinci ga al’ummar Garin Dikwa.
An bai wa mata 23,000 naira dubu biyar ga kowace mace daga cikin jumullar kudi naira miliyan 115, yayin da aka bai wa magidanta 11,000 buhun shinkafa da na wake da masara da jarkar man gyaɗa ga duk mutum ɗaya.
Rabon kuɗaɗen da kayan abincin wani ƙoƙari ne na taimaka wa al’ummomin da rikicin Boko Haram ya sa suka kasa yin noma da harkokin kasuwanci.
Voice of Borno……