Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi kira da a daina kai wa ƙabilar Fulani da ba su ji ba su gani ba a yankin kudu maso gabas da kudu maso yamma da kuma kudu maso kudancin ƙasar hare-hare.
Gwamnonin sun bayyana cewa ba daidai ba ne a riƙa kai hari ga Fulanin da ba su ji ba su gani ba.
Kazalika sun buƙaci a riƙa miƙa wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka hannun hukuma a maimakon daukar doka a hannu.
To sai dai takwarorinsu na Kudu maso Yammacin ƙasar sun yi martani, inda suka buƙaci shugabanni a yankin arewa da su ja kunnen yan ƙabilar Fulani da ke kai hare-hare a can.
Tun a watan jiya rikici ke ƙoƙarin ɓarkewa a kudu maso gabashin kasar, bayan fitar wani hoton bidiyo da aka ce na wasu Fulani ne da aka tarwatsa musu matsugunansu.
A cikin bidiyon akwai muryar wani da ke iƙirarin cewa shi ɗan yankin ne, wanda yake cewa sun yanke shawarar fatattakar Fulanin ne saboda suna barazana ga tsaron yankin.
Su dai gwamnonin na Arewa sun fake da kundin tsarin mulkin ƙasa ne, wanda ya ba duk wani ɗan ƙasa damar zama a kowane bangare yake so ba tare da wani ya hantare shi ko ya muzguna masa ba.
A ta bakin shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin ƙasar ta ‘Northern Governors Forum’ kuma gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong, ya ce NGF ba ta jin dadin yadda gwamnoni a shiyar Kudu ke tunkarar matsalar ba.
A cewarsa “yayin da ake fuskantar wani yanayi na damuwa da rashin tabbas, ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya na kira da a zauna lafiya.”
Ya ƙara da cewa ”ba dai dai ba ne a riƙa jam’i ko kuma ɓata sunan wata ƙabila saboda aikin wasu ƙalilan daga cikin ƴaƴanta”.
NGF ta kuma ce babbar fargabar da ta ke da ita a yanzu bai fi irin yadda ƙasar dama ke cikin mawuyacin hali ba, kuma ta’azzara rikici a yankin kudanci mummunar barazana ce ga haɗin kanta.
Duk da cewa wannan matsala ce da ta shafi tsaro, masana na cewa tana iya fantsama ta shafi dangantakar siyasa, musamman ma kawancen da ke tsakanin shiyyar kudu maso yamma da kuma arewacin Najeriya.
Kazalika da dama na ganin an so makara wurin shawo kan lamarin, amma ana fata gwamnonin kasar da ma sauran masu ruwa da tsaki za su jajirce wurin ganin sun shawo kan lamarin, wanda idan ba a yi hattara ba zai haifar da tsamin dangantaka tsakanin ɓangarorin kasar biyu.
Idan za a iya tunawa a watan jiya ne gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredelu ya umurci Fulani makiyaya da ke dajin jiharsa da su tattara inasu-inasu su bar yankin.
Kuma tun daga lokacin ne ake cacar baka kan lamarin a tsakanin masu fada aji daga yankunan Arewaci da kuma kudancin ƙasar, inda ake zargin muzgunawa ƙabilar Fulani makiyaya da ke dazukan kudancin ƙasar.