Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabon dokan daurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona.
Shugaban kasan ya rattafa hannunsa dokar a Abuja, ranar Laraba. Kamar yadda dokar killata, sashe 34 na sabon dokan ya tanada, duk wanda ya saba, za’a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.
Me dokar ta kunsa?
“Dokar ta kunshi baiwa juna tazara a dukkan taruka, yayinda dukkan wadanda zasu kasance a wajen su sanya takunkumin rufe fuska, su wanke hannayensu, kuma a duba zafin jikinsu kafin su shiga
Hakazalika dokar ta tanadi kada a samu mutane sama da 50 a waje guda, illa wuraren Ibada.
































