Rahotanni daga Jalingo babban birnin Jihar Taraba na bayyana cewar wasu ‘yan Bindiga waɗanda ba’a san ko su wanene ba sun sace dan majalisar dokokin jihar Barista Bashir Muhammad a daren jiya.
Da misalin kusan karfe 1:45, Yan bindigar suka yi garkuwa da Dan majalisar Barista Bashir Mohammed, mai wakiltar Nguroje a Majalisar Dokokin Jihar Taraba.
Da yake bayyanawa manema labaru shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, kuma Dan’uwa ga Dan majalisar wanda rahoton ya buye sunan sa, ya ce an ɗauke shi ne a gidansa da ke kusa da Filin Idi na Dr Jalo a garin Jalingo.
Kafar turanci ta Channels ta ce Mutumin ya bayyana cewa babu alamun jami’an tsaro a lokacin da ‘yan bindigar suka je tafiya da shi, wanda aka yi kusan awa uku ana artabu.