Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu wani dan kasar da za’a sauya shi wajen rarrabawa da kuma yin allurar rigakafin cutar corona a lokacin da rigakafin ya iso kasar.
Tuni bangaren zartarwa na gwamnati ta gabatar da kudirin Naira biliyan 400 a gaban Majalisar dokoki ta kasa da nufin sayen alluran rigakafin da za’a yi kyauta ga ‘yan Nijeriya.
Batun yin allurar Rigakafin CORONA na cigaba da ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, inda wasu jama’a ke nuna goyon baya a yayin da wasu jama’ar ke suka, inda suke ganin ba wannan ba ne abin da ya dami jama’a a yanzu.
Tuni dai wasu manyan kasashen duniya suka amince tare da fara aiwatar da allurar Rigakafin ga ‘yan kasar ta su, ƙasashe irin su Amurka da Saudiyya suna kan gaba wajen fara amfani da allurar.