A yau Litinin ne ake tsammanin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai naɗa sabon Sufeto Janar na ‘yan sandan ƙasar yayin da Sufeto Mohammed Adamu ke yin ritaya daga aiki a yau ɗin.
Mohammed Adamu zai cika shekara 35 da fara aikin ɗan sanda, inda ya fara aikin ranar 2 ga watan Fabarairun 1986.
An naɗa shi a matsayin Sufeto Janar a watan Janairun 2019 kuma zai cika shekara 60 da haihuwa ranar 17 ga watan Satumba.
Kazalika, loƙacin ritaya na wasu manyan jami’an ‘yan sanda 13 ya yi, waɗanda suka haɗa da DIG guda uku da kuma AIG guda 10.
Sai dai Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa Shugaba Buhari damar tsawaita zaman sufeto janar na ‘yan sandan idan yana da niyyar yin hakan.
Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Mohammed Maigari Dingyadi ya gabatar wa Buhari jerin sunayen wasu mataimakan sufeto janar (DIG) domin zaɓar sabon sufeton daga cikinsu.