Sojojin Hadin Gwiwa sun Hallaka Yan Kungiyar Boko Haram 200 A Garin Kalamukdo
Rahotan damuke samu jaridar HD press nacewa daga garin Kalamukdo dake Banki Karamar Hukumar Bama Ta Jihar borno na cewa sojojin hadin gwiwar kasashen Najeriya, Nijar, kamaru da Chadi sunyi gagarumin nasara kan Kungiyar boko Haram masu ikirarin jihadi.
Nasarar na zuwa ne kasada kwanaki biyar inda sojojin Najeriya sunce sunyi luguden wuta a wani sashin dajin sambisa wanda ake wa lakabi da tumbukku.
Wannan harin itace hari mafi muni da ake sammanin dakarun Hadin Gwiwar kasashen suka yi a cikin wannan shekarar.
Ruhoton yacigaba da cewa editan jaridar HD Press Yusuf Abacha yana daya daga cikin tawagar yan jaridu a Tafkin chadi yace:- sojojin sun kuma yin nasarar Cafke wasu komandojin Kungiyar boko ta Haramun.
Har izuwa yanzu Kungiyar boko Haram bata musanta wannan lamarin ba.