‘Yan bindiga masu tarin yawa sun cimma ajalinsu sakamakon samamen tudu da na jiragen yaki da soji suka kai musu a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a jihar Kaduna, Vanguard ta wallafa. Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya ce dakarun sun tabbatar da samamen da suka kai a ranar Litinin a Albasu, Rahama, Sabon Birni, Rikau, Fadama kanauta, Galadimawa, Kaya, Kidandan, Yadi, Dogon Dawa, Ngede Allah, Damari, Saulawa, Takama, Kuduru, Ungwan Yakoda babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.
“Hakazalika, a titin da ya hada Kuduru da Ugwan Yako, an ga ‘yan bindiga tare da shanun sata kuma an halaka su. “Sauran yankunan da aka duba an ga lafiya kalau sannan dakarun tudu sun duba yankunan kuma babu ‘yan bindigan,” yace. Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna gamsuwarsa a kan nasarar da ake samu tare da jinjinawa dakarun a kan yadda suke kokarin ganin bayan ‘yan bindiga. Gwamnan ya yi kira ga ‘yan jihar da su bada goyon baya ta hanyar bayyana duk wasu al’amuran ‘yan bindigar ga jami’an tsaro.