Wani coci a birnin Berlin na ƙasar Jamus ya buɗe ƙofofinsa ga ɗaruruwan Musulmai, waɗanda suka gaza shiga masallancinsu saboda dokar nesa-nesa da juna domin gudanar da sallar Juma’a a ƙarshen watan Ramadan.
A farkon wannan wata ne aka ɗage matakan da aka sanya wa wuraren ibada a Jamus, sai dai masallacin Dar Assalam da ke babban birnin ƙasar na iya cin mutum 50 ne kawai a ƙarƙashin sabbin ƙa’idoji.
Kan haka ne cocin St Martha da ke kusa ta yi tayin karɓar masallatan.
Limamin masallacin Dar Assalam ya faɗa wa Reuters cewa: “Abin farin ciki ne musamman a irin wannan lokaci na annoba ga kuma watan Ramadan. Wannan annoba ta mayar da mu al’umma guda ɗaya.”
“Wannan baƙon abu ne saboda kaɗe-kaɗe da kuma hotuna,” a cewar Samer Hamdoun, wani da ya yi sallah a cikin cocin.
Mutum fiye da 179,710 ne suka kamu da korona a Jamus, inda 8,241suka mutu – abin da ya sa ta zama ta takwas a yawan masu cutar a duniya.
[covid-data]