Alkalin wata babban Kotu da ke zamanta a birnin Zariya, jihar Kaduna ya dage sauraren shari’ar nadin sabon Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli har ya zuwa ranar 2 ga Nuwamba na wannan shekara.
A yayin zaman shari’ar, lauyan gwamnatin jihar Kaduna Barista Sunusi Usman ya kalubalanci ikon kotun na sauraron shari’ar tun da farkon al’amari.
Amma mai kara, Iyan Zazzau ya bukaci kotun da ta hana gwamnan Kaduna mu’amala da wani a matsayin Sarkin Zazzau har sai an kammala shari’ar.
Alkali Kabir Dabo na jihar Kaduna, wanda ke zama a babbar kotun Zariya, ya daga shari’ar zuwa 2 ga watan Nuwamba, don jin ƙorafin farko da gwamnatin jihar Kaduna zatayi akan ikon kotu wurin zaben sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli.
Bayan sauraron shari’ar a ranar Talata, Lauyan gwamnatin jihar, Sunusi Usman, ya kalubalanci ikon kotun wurin sauraro da yanke hukunci.
Usman, wanda shine shugaban lauyoyin gwamnatin jihar, ya sanar da kotu cewa ya rubuto duk kalubalen da yake da su a kan hukuncin kotun a ranar 26 ga watan Oktoba, kuma ya kawo wa wadanda suke kara a ranar 27 ga watan Oktoba.
Lauya mai kare mai ƙara, Yunus Usman, SAN, ya roki kotu da ta bayar da damar jin ta bakin bangarori biyu kafin ta yanke hukunci, domin samun dacewa da daidai.
Idan ba a manta ba, an yi wancan zaman kotun a ranar 19 ga watan Oktoba, Alkalin ya umarci duk wadanda ake kara a mika musu sammaci. Kamar yadda Bashir Aminu, wanda ke kara ya bukaci kotun, ya roketa da ta hana gwamnan jihar Kaduna wata mu’amala ko kiran wani sarkin Zazzau har sai lokacin da aka kammala shari’ar.