Mai Shari’a Muhammad Tukur na babbar kotun jihar Kaduna a yau 24 ga watan Nuwamba ya yankewa Maryam Muhammad Jallo da Rukaiya Muhammad Jallo hukuncin shekaru goma a gidan yari kan laifukan da suka shafi cin amana.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce ta gurfanar da masu lefin a gaban kuliya kamar yadda suka walafa a shafinsu na twitter.
Court Jails Sisters 10 Years imprisonment
Justice Muhammad Tukur of State High Court, Kaduna today November 24, convicted and sentenced the duo of Maryam Muhammad Jallo and Rukaiya Muhammad Jallo to ten years imprisonment for offences that border on criminal breach of trust. pic.twitter.com/y232fKHT6W
— EFCC Nigeria (@officialEFCC) November 24, 2020
‘Yan uwan sun yi amfani da dandalin sada zumunta na facebook wajen neman gudummawa daga masu bayarwa kuma ana tuhumar su da damfarar wani Alhaji Badamasi Shanono ta hanyar amfani da gidauniya mai suna JAMAL HEALTH FOUNDATION kamar yadda Daily Episode ta tattara.
Maryam da Rukaiya suna amfani da gidauniyar don nemama Usman Umar wanda ya kwanta sama da shekara biyu ya na fama da nakasa.
Alhaji Badamasi Shanono ya ba da gudummawar miliyan guda ga gidauniyar, yayin da wata mata ta bada dubu dari bakwai, Amma wanda ake zargi sunki mika kudaden ga mara lafiyar (Usman Umar) yayinda suka sauya kudin zuwa amfanin kansu.
Maryam da Rukayya sun amsa ‘mai laifin su Sakamakon haka, Mai Shari’a Tukur ya yanke musu hukuncin shekaru goma a kurkuku tare da zabin tarar N100,000 (Naira Dubu Dari).