Kwamishinan ayyukan jihar katsina Alh Tasi’u Dahiru Dandagoro, Yafito fili ya bayyana ma duniya yadda assusun banki sa yake a gaban manema labarai, inda kwamishinan ya karyata Alh Mahadi Shehu akan bayanan da suketa
Kwamishinan ya bayyana hakan a tattaunawar shi da manema labarai da sanyin safiyar yau 6/7/2020 da misalin karfe 10:30 a ofishin Shi dake sakatariyar gwamnatin jihar.
Kwamishinan ya tattaro cikakkun bayanan banki nashi tun daga karshen shekarar dubu biyu da sha bakwai zuwa zuwa karshen shekarar dubu biyu da sha takwas babu kudin da mahadi yace sun shiga acikin asusun ajiyar na kwamishina.
Kwamishinan ya lika takardun bayanan ajiyar nashi ga Allo agaban manema labarai.