Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa al’ummar jahar Kano daman gudanar da sallolin Juma’a tare da sallar Idi, duk da dokar zaman gida da gwamnatin tarayya ta sanya.
Babban mashawarcin gwamnan a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu.
Yakasai yace gwamnatin ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar tattaunawa da ta yi da manyan Malamai guda 30 daga bangarorin Musulunci daban daban a fadar gwamnatin. Ganduje
Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Daga karshe gwamnan ya amince da shawarwarin da aka yanke wurin, don haka ya amince za’a cigaba da dokar zaman gida, kuma za’a cigaba da dage dokar a ranakun Litinin da Alhamis.