Babban bankin Najeriya CBN yayi hasashen cewa darajar kudin kasar na Naira za ta sake karyewa a farkon sabuwar shekarar dake tafe.
Bankin Najeriyar yace hasashen na kunshe a binciken da sashin na kididdiga ya gudanar, daga ranar 7 zuwa 11 ga watan Disambar nan, inda ya tuntubi kamfanoni da daidaikun ‘yan kasuwa akalla dubu 1.
A makwannin baya bayan nan, darajar Naira ta yi faduwa mafi muni a ranar 30 ga watan Nuwamba, lokacin da canjin dala 1 ya tashi kan Nairar 500. Tun daga lokacin ne kuma darajar Nairar ke hawa da sauka a tsakanin 460 zuwa 470 kan dala 1.
A dai karshen watan na Nuwamba ne Najeriya ta fada matsin tattalin arziki karo na biyu cikin shekaru 5.


































