Muhawara ta kaure a Najeriya bayan wasu alamu sun nuna cewa da wuya Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama gayyatar da majalisar wakilai ta yi masa domin ya je ya yi bayani a kan taɓarbarewar tsaro.
A ranar Alhamis ne ake sa ran Shugaba Buhari zai je gaban majalisar, sakamakon gayyatar da ta masa a makon jiya, bayan yankan ragon da mayaƙan Boko Haram suka yi wa wasu manoma a ƙauyen Zabarmari da ke jihar Borno.
Da farko fadar shugaban ƙasar ta ce ya amince da gayyatar, amma daga baya sai ministan shari’ar Najeriya ya ce majalisar ba ta da hurumin gayyatarsa.
Ra’ayi dai ya bambanta a tsakanin ƴan ƙasar bayan sun fahimci cewa Shugaba Buhari zai iya mayar wa ƴan majalisar dokokin ƙasar goron gayyatar da suka tura masa kan matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar.
Fa’ida
Tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya, Sani Zoro na da ra’ayin cewa zuwan shugaban ƙasar na da fa’ida, saboda za ta ba shi damar nuna wa ƴan majalisar irin ƙalubalen da yake fuskanta ta yadda zai nemi haɗin kansu domin a gudu tare a tsira tare.
“Dama ce gagaruma kowa ya san ƙasar nan na cikin yaki, idan kuma ana yaki sai ka yi aiki da majalisa ka jingine komai domin samun ɓullewa”, in ji Zoro.
Sani Zorro ya ce shugaba ƙasar zai iya amfani da damar wajen neman amincewar ƴan majalisar domin rage wa gwamnati ɗawainiya, ta hanyar bai wa kamfanoni damar kammala wasu manyan ayyuka.
Tsohon ɗan majalisar ya bayar da misali da aikin gina hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano, da Gadar Niger Bridge da hanyar da ta tashi daga Legas ta dangane da Ibadan da dai sauransu, domin su kammalu, kana su fid da kudinsu ta hanyar karɓar haraji daga masu abin hawa kamar yadda ake yi a sassan duniya.
Sai dai kuma wasu ƴan siyasa kamar su Sha’aban Ibrahim Sharada na ganin cewa bai kamata Shugaba Buhari ya je zauren majalisar ba.
Sha`aban Sharada, ɗan majalisar wakilai a Najeriyar ya ce da ƴan ƙasar sun san irin aikin da Buhari yake a fannin tsaro da ba za su nuna goyon-bayan gayyartarsa ba.
Tozarci
Tun lokacin da fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya amince da gayyatar da majalisar wakilan ta yi masa, bayanai daban-daban ke fitowa da nuna cewa an shiga ƙila-wa-ƙala, wato da wuya ya karrama gayyatar.
Akwai rahotannin da ke cewa wasu gwamnoni na adawa da zuwan nasa, saboda a cewar su zai buɗe wata hanyar da ba za ta bulle ba, wato majalisun dokoki a matakin jiha ka iya ara su yafa su dinga saka su a gaba suna gayyata a kan abin da bai taka kara ya karya ba.
Wata ruwayar kuma cewa ta yi ƴan majalisar dokokin Najeriyar, musamman ƴan jam`iyyar APC mai mulki da dama na fargabar cewa watakila za a tozarta shugaban ƙasar, don haka ba sa goyon bayan zuwansa.
Zaman haɗin-gwiwa
Sai dai kuma abin da masu lura da al’amura ke cewa shi ne da ma ƴan majalisar ba su yi niyyar gayyatar shugaba Buhari ba.
A cewar masana dama ƴan majalisar dattawa ba su yanke wannan shawarar a zaurensu ba, amma kuma aka fito ana cewa za su yi zaman haɗin gwiwa da takwarorinsu wajen karɓar shugaban ƙasar.
Kuma ana haka sai ministan shari`a Abubakar Malami ya yi mai gaba ɗaya, wai haihuwa da hanji, in ji ƴan magana ya dogara da kundin tsarin mulkin ƙasar yana cewa “ƴan majalisar ba su da hurumin titsiye shugaban ƙasa domin ya yi bayani a kan dabarun yaki saboda abu ne na sirri”.
Abin da Kundin tsarin ƙasa ya ce
Masanan harkokin shari’a kamar Barrister Bulama Bukarti na cewa zance da ministan shari’a’ya yi dai-dai da shara, domin babu gaskiya cikin maganganunsa.
Barrister Bulama ya ce sashi na 88 da 89 na kundin tsarin mulki, ya bai wa majalisar dattawa ko wakilai damar gayyatar kowa ko hukuma ko da shugaban ƙasa ne.
Don haka a matsayin shugaban ƙasa da haƙƙi ƴan ƙasa ya rayata a wuyansa wajen kare su da dukiyoyi, majalisa na da ƙarfin ikon gayyatarsa domin amsa tambayoyinta.
Kuma bijirewa sammacin majalisa dai-dai yake da karya dokokin kundin tsarin mulkin ƙasa, in ji Bukarti.
Karin bayyani
Ƴan Najeriya da dama dai ba su damu da irin wannan kwan-gaba-kwan-baya ko kulli-kucciyar ba. Abin da ya fi damun ƴan ƙasar shi ne a yi kowanne irin siddabaru, a gaggauta inganta tsaro da zaman lafiya ya dawwama a ƙasa.