Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan ya ce babu wani mutum da ke karkashin gwamnati da ya fi karfin majalisar dokokin kasar ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi.
Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis.
A sakon da ya wallafa a Twitter, Sanata Lawan ya ce: “lokacin da muke tashi daga zaman majalisa na jiya na yi magana kan bukatar da ke akwai ga mutanen da shugaban kasa ya nada kan mukamai su guji ce-ce-ku-ce na babu gaira babu dalili da kwamitocin majalisun dokoki domin kuwa babu wanda ya wuce majalisa ta yi bincike a kansa.”
Ya kara da cewa kwamitocin majalisar suna gayyatar hukumomin gwamnati ne domin gudanar da ayyukan da al’umma suka aike su majalisun su yi kamar yadda tsarin mulkin shekarar 1999 ya gindaya.
A baya bayan nan dai ana samun takun saka tsakanin ministoci da ‘yan majalisa, inda ko a makon da muke ciki sai da ministan yankin Naija Delta Godswill Akpabio ya yi zargin cewa ‘yan majalisar suna samun kaso mai tsoka na kwangilolin da ma’aikatarsa ke bayarwa, lamarin da ya harzuka ‘yan majalisar.
A farkon watan nan, minista a ma’aikatar kwadago ya kai ruwa rana da ‘yan majalisar game da zargin tsoma bakinsu a kan shirin shugaban kasar na bai wa matasa aikin yi wanda aka fi sani da N-Power.
Masu lura da lamura na ganin wannan takaddama d ke tsakanin bangarorin biyu abin kunya ne ganin cewa ‘yan majalisar da bangaren zartarwa abokan juna ne ta fannin siyasa, sabanin majalisar da ta gabace ta, wacce ake ganin ta hana ruwa gudu a gwamnatin Shugaba Buhari.
Ga abunda yace a shafinsa na twitter
https://twitter.com/DrAhmadLawan/status/1286159003282821124