A yayin da ake ta samun rahotannin mace-macen mutane a sassa daban-daban na arewacin Najeriya, wasu makiyaya sun ce su ma dabbobi na mutuwa barkatai a halin yanzu a wasu sassan yankin.
Shugaban kungiyar matasa makiyaya na shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar, Abdurrahman Buba Kwacham, ya shaida wa BBC cewa, sai da suka gudanar da bincike sannan suka gano cewa a yanzu haka ana asarar dabbobi na fitar hankali.
Ya ce, dalili kuwa shi ne mutane sun kiwota dabbobi masu yawa na tsawon lokaci amma idan sun je kasuwa domin su siyar ba bu kasuwa, sannan kuma su masu dabbobin ba su da wadataccen abincin da zasu rinka ba wa dabbobin.
Abdurrahman Buba Kwacham, ya ce ” Ba zan iya cewa ga adadin dabbobin da suka mutu ba musamman a jihohin Adamawa da Zamfara da Kano da Jigawa da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna, Allah ne kadai ya san adadinsu”.