Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta tabbatar da sace masallata 18 da kashe mutum biyar yayin da ake gudanar da Sallar Juma’a a garin Dutsin Gari da ke Ƙaramar Hukumar Kanoma a jihar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar SP Muhammed Shehu ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun saje da masallatan inda a lokacin da ake shirye-shiryen sallar suka gudanar da wannan aika-aikar.
A cewarsa, “bayan ‘yan bindigan sun tarwatsa masallatan, sai suka kwashi wasu suka yi daji da su, sannan a cikin harbin da suka yi, mutum biyu suka rasa rayukansu, amma kuma daga baya cikin waɗanda suka ji rauni mutum uku sun rasu, wanda hakan ya sa suka zama biyar”.
Wasu mazauna ƙauyen sun bayyana cewa masallata 40 ne aka sace, ciki har da limamin masallacin, amma dai rundunar ‘yan sanda reshen jihar ta kafe cewa mutum 18 ne aka sace, kuma ban da liman a cikinsu.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun shiga ƙauyen kan babura sama da 100 saɓanin yadda SP Shehu ya shaida mana cewa ‘yan bindigar sun saje ne da masallata.
SP Shehu ya bayyana cewa tuni jami’an tsaro suka shiga neman waɗanda aka sace da kuma shirye-shiryen kare afkuwar lamarin a nan gaba.
Ko a kwanakin baya sai da ‘yan bindiga suka sace ‘yan sanda 12 a jihar Katsina kan hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara daga jihar Borno, haka kuma suka kashe aƙalla mutum 16 a wasu yankuna na jihar Kaduna.
Haka kuma a ranar Asabar ma sai da ‘yan bindigan suka sace shugaban Jam’iyyar APC reshen jihar Nasarawa, Mista Philip Tatari Shekwo.