Bayanai sun bayyana yadda aka kama Abdulrasheed Abdullahi Maina, a kasar jamhuriyyar Nijar bayan shafe tsawon lokaci ana neman shi a cikin Najeriya, ta hanyar shigar burtu da ɓadda kama da yin takardun bogi.
Jami’an ‘yan sanda a karkashin jagorancin CP Garba Baba Umar ne su ka kutsa har babban birnin Niamey a kasar Nijar, su ka cafke Maina.
An yi nasarar kama Malam Abdulrasheed Abdullahi Maina ne a ofishin jakadancin kasar Amurka da ke Niamey, inda ya yi karyar shi mutumin Amurka ne.
Abdulrasheed Maina ya yi takardun bogi ne da su ka ba shi damar labewa a Jamhuriyyar Nijar. Bayan haka, rahoto ya nuna cewa tsohon jami’in gwamnatin ya rika amfani da waya kirar Thuraya ne domin jami’an tsaro su gagara gane inda ya labe.
Duk da wannan dabaru, ‘yan sandan Najeriya ba su gagara gano Malam Maina ba, su ka cafke shi, kuma su ka dawo da shi domin cigaba da shari’arsa a kotu.
Abdulrasheed Maina ya boye a Nijar ne bayan Alkali ya sa a karbe takardunsa, sai da ya ajiye fasfon Najeriyarsa da na Amurka kafin ya iya samun beli.
Maina ya yi amfani da babur ne, ya faki idanun jami’an da ke kan iyakokin Najeriya a jihar Sokoto, ya tsere zuwa Nijar, a karshe ya sake shiga hannun hukuma.
Bayan abin nan ya faru, kun ji cewa Sanata Ali Ndume wanda ya tsaya wa Maina, ya umarci lauyoyinsa su fara shirye-shiryen zame shi daga shari’arsa. Sanatan na jihar Borno, Ali Ndume ya yi kwanaki biyar a garkame a kurkuku a sakamakon tsaya wa Maina da yayi, shi kuwa ya tsere ya bar shi a tashin hankali.
A halin yanzu Alkali ya bukaci a adana Abdulrasheed Maina a gidan yari har sai an gama shari’a.