- Yazama Dole mu hukunta Duk Wani Bafulatanin da Aka Samu Da Aikata Laifuffuka Acikin Najeriya.
Inji Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Wato Jama,a Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya Nesanta kansa daga aika-aikar wasu fulani Acikin Najeriya.
Kamar Yadda Muka Samu Labari Daga Majiyar Mu Cewa Shugaba Buhari yace ba ya goyon bayan garkuwa da mutane da Hallaka Jama,a Tare Da barnar Da Wasu fulani keyi Acikin Najeriya.
Adaidai Lokacin Da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Ke Wannan Jawabin ya Umarci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Karkashin Shugaban `Yan Sandan IGP Adamu Muhammad Abubakar da ya bayyana Sunayen Fulanin da ake shari’a da su a kotu Akan Zargin Su Da Aikata Laifin Garkuwa Da Mutane Kwashe Dukiyar Al,ummar Hallaka Jama,a Acikin Najeriya Domin Gaggauta Zantar Masu da Hukunci Mai tsuri Acikin Najeriya.
Majiyar Mu Ta sanar Mana Da Cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Yayi Wannan Umarnin Ne Ajiya Litinin 15 ga Watan February 2021 Inda Yake Cewa Lallai Yazama Dole Gwamnatin Shi ta Hukunta Duk Wani Wanda Aka Kama da Laifin cin Amanar Tsaron Najeriya.
Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan sandan Najeriya su fito da sunayen duk Fulanin da ake zargi da laifi Domin Tabbatar Da Cewa Hukunci Yahau Kan Shi.
Shugaban ya umarci jami’an ‘yan sanda da su wallafa sunayen gaba daya makiyaya Fulanin da ake shari’a da su a kotu da zargin aikata laifuffuka.
Kamar yadda Majiyar Mu Ta Labarta Mana Cewa, shugaban kasar ya bada wannan umarni ne domin nuna babu hannunsa a wajen wanke makiyaya Fulani Acikin Najeriya.
Wato Jama,a idan Kuntuna Ana zargin mai girma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da yi wa ta’adin Fulani rufa-rufa saboda kabilarsu daya.
Mai ba shugaban kasar shawara wajen yada labarai, Garba Shehu ne ya bayyana wannan a lokacin da aka yi hira da shi a shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels TV.
Garba Shehu Ya ce Shugaba Buhari ya damu iya damu wa a kan halin da ake ciki, ya na sane cewa nauyin gwamnati ne ta tsare rayukan al’umma Sannan Kuma ta kawo karshen rikicin da ake yi, daga garkuwa da mutane zuwa sababbin laifuffukan da ake yi na fadan kabilanci.
Acewar Garba Shehu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Ba ya tare da Duk Wani Bafulatanin Da Yakangare Sannan, ba ya goyon bayan Ayyukan Rashin Gaskiya, inji Shugaba Buhari.
Muna Rokon Ubangiji Allah Ya Zaunar Mana Da Kasar Mu Najeriya Da.